Pulse.ng logo
Go

Sani Idris "Moda" Ina nan da raina ban mutu ba

An samu labari wanda ya yadu a kafafen sada zumunta mai cewa asibitin da yake jinya ta sanar da mutuwar sa

  • Published:
Sani Idris Moda play

Sani Idris Moda

(Instagram/northern_hibiscuss)

Shahararen jarumin fina-finan hausa, Sani Moda wanda ke fama da rashin lafiya ya karyata jita-jita dake yaduwa na cewa ya mutu.

An samu labari wanda ya yadu a kafafen sada zumunta mai cewa asibitin da yake jinya ta sanar da mutuwar sa.

Jaruma Saratu Gidado ta kai masa ziyara a asibitin da yake jinya play

Jaruma Saratu Gidado ta kai masa ziyara a asibitin da yake jinya

(Instagram/saratudaso)

Ya shaida ma jaridar Rariya cewa yana nan da ran sa, sai dai yana barar addu'a daga jama'a na samun sauki cikin gaggawa.

Kamar yadda wasu abokan sana'ar shio suka sanar, asibitin tayi kuskuren sanar da sunan shi a maimakon na kusa da gadon da ya kwance wanda ya rasu a daren ranar litinin.

Jarumin yana kwance a asibitin Barau Dikko dake nan garin Kaduna inda yake jinyar ciwon suga.

A karshen mako da ya shude, jaruma Saratu Gidado wacce aka sani da Daso ta kai masa ziyara a asibitin da yake kwance. Banda ita, sauran jarumai da masu ruwa da tsaki na kannywood sun kai masa ziyara domin duba lafiyar sa.

 

Kan rashin lafiyar shi, shahararen kafar watsa labarai, Northern Hibiscuss ta bude assusun agaji domin kai masa dauki.

Jarumin shirin 'Wasila' yana daya daga cikin jarumai da suka taka rawar gani a masana'antar fim kana yana daya daga cikin tsofafin yan fim da suka raya Kannywood.
 

 

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.