Wani basarake da ya musulunta kwanan baya ya roki jama'a da su garzaya gidan shi domin neman auren yayan shi mata balagaggu da wasu matayenshi.
Basarake wanda ya musulunta kwanan baya na neman wadanda zasu auri yan matan gidan sa
Dauda Auta wanda yake basaraken gargajiya na kabilar Gwari na jihar Kaduna ya musulunta ne a masallacin sultan Bello yayin da shahararren malami Sheikh Ahmad Gumi ke gudanar da tafsir.
Dauda Auta wanda yake basaraken gargajiya na kabilar Gwari na jihar Kaduna ya musulunta ne a masallacin sultan Bello yayin da shahararren malami Sheikh Ahmad Gumi ke gudanar da tafsir.
A jawabin da yayi bayan ya amshi musulunci yana mai cewa "Ina Da Mata 11 Da 'Ya'ya 44 Kuma Mafiyawancin Su Mata Ne, Ina Kira Ga Matasa Musulmi Da Su Taimaka Mini Su Je Gidana Neman Aure Domin Kwashe Balagaggun 'Ya'yana Mata, Allah Taimaki Musulmi".
Don haka yayi kira ga musulmai masu niyyar yin aure da garzaya gidansa.
Yayi la'akari da sharudan dake tare da addinin musulunci wanda ya ba musulmin auren mata hudu kacal.
Muna fatan Allah ya hada matan sa da yayan sa da mazaje na gari.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng