Shugaban huƙumar yaki da cin hanci da rashawa na kasar nijeriya yayi kira da a kafa kurkuku a dajin sambisa don tsare masu aikata laifin zurmiya da cin hanci.
‘Ya kamata a dinga ɗaure barayin gwamnati a dajin sambisa’ - inji Magu
Shugabar huƙumar EFCC yayi kira da a kafa kurkuku a dajin sambisa don tsare masu laifin cin hanci da rashawa
Bisa ga labarin da BBC hausa ta fitar, shugaban huƙumar yayi kiran lokacin da ake bikin bude offishin shiyya na huƙumar a kaduna.
Dajin sambisa maboya ce ta mayakan Boko haram a jihar Borno dake arewa maso gabas na kasar.
“Muna kira da a kafa wata kurkuku a dajin sambisa don kawar da masu laifukan cin hanci da rashawa daga cikin mu” inji shugaban hukumar.
Magu yayi kira ga bangaren shari’a da ta mara yunkurin gwamnatin tarayya wajen yaki da rashawa
“Dole mu canza lamarin da mu zage dumtsi wajen yakin masu neman gurgunta nasarar da muke samu’ yace.
Ya kara da cewa, “ dole mu hada karfi wuri guda don wankar da cin hanci da rashawa kafin ya kashe mu”.
A karshe Magu ya yi wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai yabo don taimakon da ya ba huƙumar wajen bude offishin shiyya a jihar.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng