A ranar Talata ga watan Nuwamba, mun karɓi rahoto game da rasuwar Tsóhon Sarkin Musulmi na goma sha takwas. An binne shi daidai da sharuddan musulunci a Hubbaren Shehu, Garin Sakkwato.

A cikin taʼaziya wanda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya aika ma Alʼummah ta hannun Wakilinsa Imam Imam, ya báyyana cêwa Dasuƙi shi ne ɗaya daga cikin matukar aiwatan canji domin ci gaba na Alʼummah. Ya tura duka ilmin sa da kuma ƙwarewansa ga shaʼanin musulunci domin ci gaba na Iyali, Alʼummah da kuma Najeriya gaba ɗaya.  Da yake taʼaziya, Tambuwal ya ce:

"Tarihin ƙananan hukumomi na Najeriya ba zai háɗu ba idan ba tare da an yi lissáfin babban ayyuka na Sultan Dasuƙi. Yana cikin waɗanda sun yi jagora domin ƙadamar da tsárin gwamnati a Najeriya. Ya zauna a kan kujera na Sarki hár tsawon shekaru takwas, kuma ya bada goyon baya akan aukuwan ilmi na mata da yara a kowane ɓangaren Najeriya".

" Ya tabattar da ƙarin ilmi na Malamai akan Karatun addini Musulunci. Za mu tuna da ayyuka na ingantar da zaman lafiya tsakanin mutane masu addini daban-daban, da kuma mutunci tsakanin mutanen yarurukka daban-daban.”

Bugu da ƙari, Dasuƙi ya ingatar da tsari na hanawa da kuma gudanarwar rikici ko tashin-hankali tsakanin Jamiʼun Najeriya. Haƙika, shi ne ya kawo ƙarshen rikice-rikice tsakanin mutanen Tiv, Jukun, da Fulani a Jihar Taraba."

Da yake jawabi, Tambuwal ya ce;

"Muna adduʼa, muna roƙo ga Allah(SWA) ya albarkace shi da Jannatul-Firdaus."

Ya ce  mutanen Sakkwato da gwamnatin Sakkwato, za su ci gaba da ɗora muhimmanci sosai akan gudunmawar wanda marigayi ya kawo. Gwamna ya kuma miƙa gaisuwansa da haƙuri ga Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Saʼad Abubakar da kuma iyalan Marigayi Dasuƙi domin wannan rasuwan da Allah ya kawo.