Pulse.ng logo
Go

Kalli kayatattun hotunan yakin neman zaben shugaba Buhari

A cikin hotunan za'a gan inda shugaban ya sanya kayan gargajiya na manyan al'adu uku dake kasar.

  • Published:
play (Instagram/buharisallau)

Harkar siyasa da yakin neman zaben ya mamaye kasar inda yan takara na jam'iyu mabambanta dake fadin kasar ke neman cinma burin su na shugabanci.

"Our efforts were unsuccessful" – Buhari tells father of aid worker killed by Boko Haram play

President Muhammadu Buhari

(Twitter/MBuhari)

 

Bisa ga wannan yanayin da ake ciki tawagar ma'aikatan yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da wasu kayayatattun hotunan shugaban bayan jam'iyar APC ta amince da tsayawar shi.

A cikin hotunan za'a gan inda shugaban ya sanya kayan gargajiya na manyan al'adu uku dake kasar.

Kai ga yanzu shugaban shine gwanin jam'iya mai mulki, yayi nasarar zama dan takarar ta bayan da ya samu kuri'u 14,842,072 daga deliget na jam'iyar.

APC Primaries: Read Buhari's acceptance speech after being elected APC's flag-bearer play

President Buhari

(Facebook/Buhari)

 

APC ta tabbatar da haka a taron kasa da ta gudanar ranar Asabar 6 ga watan Oktoba a filin Eagle square dake nan birnin tarayya.

Shugaban zai kara da Atiku Abubakar na jam'iyar PDP da yan takarar sauran jam'iyu wajen zarcewa a saman kujerar mulki a zaben 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya doke sauran yan takarar PDP wajen zama gwanin jam'iyar bayan zaben da aka gudanar a garin Fatakwal karshen makon da ya gabata.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement