Pulse.ng logo
Go

Adamu Ciroma Dandazon jama'a sun halarci jana'izar tsohon ministan kudi(Hotuna)

An gudanar da sallar a masallacin An-nur dake nan Abuja yammacin ranar alhamis 5 ga watan Yuli.

  • Published:
An gudanar da sallar jana'izar marigayin a masallacin an-nur dake nan Abuja play

An gudanar da sallar jana'izar marigayin a masallacin an-nur dake nan Abuja

(Instagram/buharisallau)

Dandazon jama'a suka halarcin sallar jana'izar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Marigayi Adamu Ciroma, wanda ya rasu ranar alhamis.

An gudanar da sallar a masallacin An-nur dake nan Abuja yammacin ranar alhamis 5 ga watan Yuli.

Mallam Adamu Ciroma ya rasu ne a wata asibitin kudi dake nan babban birnin tarayya bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

play (Instagram/buharisallau)

 

Cikin dandazon jama'a da suka halarci jan'izar sa akwai shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Sarkin Fika, Mai martaba Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa.

Shima shugaban ma'akatan fadar shugaban kasa, Alhaji Abba Kyari ya halarci jana'izar tare da wasu ma'aikatan  fadar shugaban.

Bukola Saraki tare da gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam a wajen sallar jana'izar marigayi Adamu Ciroma play

Bukola Saraki tare da gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam a wajen sallar jana'izar marigayi Adamu Ciroma

(Instagram/buharisallau)

 

Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam tare da takwaran sa na jihar Kebbi Atiku Bagudu suma sun hallara.

Takaitaccen tarihin marigayi

Tsohon jigon jam'iyar PDP ya rasu ranar alhamis 4 ga watan Yuli kuma yana yana da shekaru 84.

Haifafen dan garin Potiskum dake jihar Yobe, shine gwamnan babban banki tsakanin watan Satumba na 1975 zuwa Yuni na 1977.

Adamu Ciroma, tsohon gwamnan CBN ya rasu play

Marigayi Adamu Ciroma ya rasu yana shekaru 84 a duniya

(Punch)

 

Bayan haka ya rike matsaayin ministan kudi karkashin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wa'adi na farko na mulkin sa.

Bugu da kari shine shugaban yakin neman zabe na Obasanjo yayin da tsohon shugaban ke neman zarcewa a zaben 2003.

Gabanin rasuwar sa, marigayin ya taka rawar gani a harkar siyasar kasar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement