Pulse.ng logo
Go

Yaran makaranta Hotunan kafin tafiya na daliban makaranta 22 da hatsari ya rutsa dasu hanyar zuwa Kano

Hotunan daliban makaranta 22 kafin tafiya wanda yayi sanadiyar ajalin su, hanyar su zuwa jihar Kano don gabatar da ziyarar neman ilimi

  • Published:
Daliban kenan kafin su gabatar da tafiyar wanda yayi sanadiyar ajalin su play

Daliban kenan kafin su gabatar da tafiyar wanda yayi sanadiyar ajalin su

Wannan shine hotunan da yaran makarantar goverment day dake Misau jihar Bauchi kenan yayin da suke shirin tafiya zuwa jihar Kano domin yin ziyarar neman ilimi.

Hotuna da suka dauka kenan tare da malaman su kafin su kama hanya zuwa jihar domin gabatar da ziyarar neman ilimi wato Excursion.

Daliban kenan kafin su gabatar da tafiyar wanda yayi sanadiyar ajalin su play

Daliban kenan kafin su gabatar da tafiyar wanda yayi sanadiyar ajalin su

 

Daliban dai basu samu damar cinma burin su ba inda suka samu mummanar hatsari wanda yayi sanadiyar mutuwar su sakamakon haduwar motar su da wata tirela a babban titin hanyar zuwa Kano.

Anyi jana'izar su a daren ranar talata a farfajiyar sarkin Bauchi.

 

Wannan mutuwar tasu ya razanar zukata inda manyan yan kasa da sauran jama'a sun nuna bakin cikin faruwar haka, ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar.

Gwamnan ya jajanta ma yan uwan wadanda suka rasu sanadiyar hatsarin mota da ya rusa dasu tare da yi masu fatan Allah ya jikan su da rahama kuma Allah ya ba yan uwan hakurin jure rashin su.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.