Pulse.ng logo
Go

Biki buduri Hotunan daga bikin auren diyar ministan shari'a

Ministan shari'a ya aurar da diyar shi Zakiya zuwa da angon ta Saifullahi Mai gishiri ranar asabar 8 ga watan Satumba a jihar Kebbi.

  • Published:
  play Amarya da ango tare da mataimakin shugaban kasa bayan an daura aure su (Instagram/Buharisallau)

Ministan shari'a Abubakar ya aurar da diyar ranar asabar bikin auren ya samu halarcin manyan masu hannu da shunu dake kasar ciki har da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

An daura auren Zakiyya Abubakar Malami da Saifullahi Mai gishiri a fadar mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Bashar.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya halarci bikin wanda aka yi a jihar Kebbi play

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya halarci bikin wanda aka yi a jihar Kebbi

(Instagram/buharisallau)

Jihar Kebbi ta samu bakoncin manyan baki da suka halarci bikin daurin auren.

Cikin bakin da suka halarci bikin akwai gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu tare da takwarorin sa na jihar Katsina, kaduna, Jigawa, Sokoto da Zamfara.

Amarya Zakiyya da angonta Saifullahi a wajen taron bikin auren su play

Amarya Zakiyya da angonta Saifullahi a wajen taron bikin auren su

(Abba villa)

Shima sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya halarci bikin tare da shugaban hukumar Kwastam da na ma'aikatar shige da fice.

play (Abba villa)

Amarya Zakiyya Abubakar Malami play

Amarya Zakiyya Abubakar Malami

Wasu daga cikin ministocin kasa da suka halarci bikin sun hada da ministan tsaro, ministan sufuri, ministan ilimi da ministan mai.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement