Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta karrama wasu daga cikin fitattun jaruman masanaantar nishadi ta kannywood mawaka da yan wasan kaikwayo.

Shahararren mawaki Abdul Amart tare da wasu mawakan Hausa suka shirya wakar 'Sakamakon canji' mai bayyana ayyukan cigaba da gwamantin buhari ta aiwatar a wa'adan sa na farko da yin mulki.

Aisha Buhari ta jinjina ma jaruman masana'antar nishadi ta Kannywood bisa ga gudummawar da suke bada wa wajen wayar da kan al'umma tare da haifar da zaman lafiya.

Ta ce ya zama dole a karramar jarumai domin rawar da suke takawa wajen cigaban gwamnati baya misaltuwa.

Taron dai ya samu halarcin shugaba Muhammadu Buhari tare da wasu manyan ma'aikatan fadar sa.

Fiattun mawaka da suka halarci taron sun hada da Naziru M.Ahmad, Aminu Ladan Abubakar (Alan waka), El-Muaz, Ado Gwanja, Nazifi Asnanic, Ali Jita, Fati nijar da sauran su.

A bangaren jaruman fim kuwa akwai  Adam A.Zango, Fati Washa, Rukayya Dawayya, Jamila umar Nagudu, Maryam Yahaya, Halima Atete, Hauwa Waraka, Fati S.U, Dan Auta, Aminu Saira, Amal Umar da Fati Shu'uma.