Pulse.ng logo
Go

Halin mayu Ana tuhumar wata mahaifiya bisa ga zargin sa ma diyar ta yaji a farji

za’a tuhume ta da aikata laifufuka uku da suka sabawa doka

  • Published:
Kotu ta daga karar zuwa 25 ga watan satumba play

Kotu ta daga karar zuwa 25 ga watan satumba

Wata yar kasuwa Mercy Segun mai shekara 42 ta shiga hannun hukuma inda ta ziyarci kotu ranar laraba 30 ga watan agusta inda ake zargin ta da dukar diyar ta har ma ta sa mata yaji a farji.

Segun ‘yar unguwar Idu gbagyi na garin Karmo dake Abuja zata fustanci tuhuma na aikata laifuffuka uku da ya kai ga raunata yar karamar yarinya.

Wanda ta gurfanar da ita a gaban alkali Mrs Florence Auhiobohi ta fada ma kotu cewa makwabciyar wanda ake tuhuma ta kai karar ta ga hukumar yan sanda dake Karmo ranar 22 ga watan agusta.

Tana zargin ta da muzguna ma diyar har ma ta sa mata yaji a farji kasancewa diyar karamar yarinya ce.

Auhioboh ta fada ma kotu cewa laifin da wanda ake zargi ta aikata ya sabawa doka kuma yayi sanadiyar raunata yarinyar.

Mai bayar da kariya ya karyata zargin da ake ma Segun.

Mai shari’a Alhaji Abubakar Sadiq ya ba Segun damar yin beli da N30,000 har zuwa ranar 25 na watan satumba da kotu zata kara zama don sauraron karar kuma.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.