ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Halin da sanata ke ciki yayin da abokan aikin sa suka kai masa ziyara a asibiti

Sai dai tsirarru daga cikin dandazon yan majalisar suka samu damar ganawa dashi bisa matakan tsaro da jami'an dake tsaran shi suka kafa

Dan majalisar wanda ya shiga hatsaniya da jami' an tsaro yana fuskantar matsin lamba bisa zargin da ake masa na daukan nauyin wasu yan tawaye a jihar Kogi.

A yayin da take gudanar da zaman ta, majalisar karkashin jagorancin Bukola Saraki ta yanke shawarar ziyartar Dino Melaye a asibitin da yake jinya domin lura da lafiyar sa.

Sai dai tsirarru daga cikin dandazon yan majalisar suka samu damar ganawa dashi bisa matakan tsaro da jami'an dake tsaran shi suka kafa.

Maganar shugaban majalisar dattawa

ADVERTISEMENT

Yayin da ya gana da manema labarai bayan yayi ido hudu da mai jinya, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana cewa, sanatan yana murmurewa kuma yana samun kulawa bakin gwargwado.

Bugu da kari shugaban ya bayyana cewa, Dino Melaye bai sa abinci a cikin sa ba na tsawon sa'o'i 24. Yace ana kokarin neman yadda za'a shawo kanshi kan yaci abinci. Ya kara da cewa kwararrun likitoci suna cigaba da kula dashi.

Saraki yace suna ma ubangiji godiya kan yadda suka samu dan majalisar duk da cewa yana fama da ciwon tari.

Daga karshe, yayi ma ma'aikatan asibitin taraya godiya bisa kokarin da suke wajen kula da lafiyar sanatan kana yana mai masa addu' ar samun sauki.

Kalaman Sanata Shehu Sani

ADVERTISEMENT

Bayan sakon da ya wallafa mai cewa, abokin aikin sa na fuskantar tuhuma bayan da ya nuna bayan sa ga gwamnatin tarayya, shima dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani yayi haske game da halin da ya gan dan majalisar.

Kamar yadda ya rubuta a shafin sa na twitter, Shehu Sani yana mai cewa " Ina daya daga cikin sanatocin da suka samu damar ganin Dino a asibitin tarayya inda yake jinya, ba'a saka masa ankwa ba, sai dai an sa mashi ruwa. Da kyar yake magana kuma an saka mashi bandaji a wuya".

Zargin da ake yi ma Dino Melaye

Hargitsin  jami'an tsaro dasanatan ya fara ne tun ranar litinin a filin jirgin saman Abuja bayan da aka hana shi tafiya kasar waje.

Dan majalisar yaki amincewa da gayatar da jami'an tsaro suka yi masa don bada amsar zargin da ake masa.

ADVERTISEMENT

Ana zargin sa da daukar nauyin wasu yan tawaye da aka kama a jihar kogi masu haifar da rikicin siyasa a jihar.

Sai dai dan majalisar ya sha musanta wannan zargin inda ya danganci lamarin da aikin siyasa daga makiyin sa.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT