Haifafiyar yar kaduna ce, mahaifinta dan kasar Saliyo ne yayin da ita kuma mahaifiyar ta yar asalin garin zazzau ce.
Tana daya daga cikin fitattun mawaka mata da ke raya kunnuwar al'umma ta hanyar waka kuma a fannin zamu iya ce tayi fice matuka.
Wani abun mamaki game da ita shine ta kasance mai dauki da juna biyu yayin shirya wani bidiyon wakar ta ba tare da sanin mafi yawancin jama'a masu kallo ba.
Ga yadda hirar mu da ita ta kasance:
Muna taya ki murna bisa karuwar da kika samu na diya a cikin watan Maris Allah shi raya.
Ameen ameen. Yara biyu kenan na farko namiji ne dan shekara hudu yanzu.
Kin sanar da cewa a cikin bidiyon wakar ki wanda kika yi da Tiwa Savage kina dauke da juna biyu a lokacin da ake shirya ta, ya kika ji a lokacin?
Wai an dandana!
Kin ba mutane mamaki, ya kika yi yadda kika shirya bidiyo ba tare da kowa ya san cewa kina dauke da ciki?
Ai ina ganin anyi maganar a kafafe sadarwa. Amma ka san ni bana amsa kowa. Ko da gaske ne ko karya kawai sai dai mutum ya jira yaji. Kasan a yanayin irin wannan lokacin kawai kana addu'a ne Allah ya sauke ka lafiya ba wai kana son yin magana. Ba wai nayi shuru ne don kada inyi magana ba, nayi ne don a lokacin tsakani na da Allah kawai.
Idan na fahimce ki, rayuwar gida daban rayuwar harkar waka ko amfani da dandalin sada zumunci suma sun bambanta kenan?
Suna aduwa, ka san yanzu an koma harkar social media. Ni a waje na sabuwa ne bawai ina yin shuru ne don kada mutane su sani.
Wata sa'i ma na kan daura hoton yara na. Da asuba wata sa'i idan na tashi nakan yi wasa da yara na kuma in daura a social media. sai ka gan ma wata rana yara na ne ke wasa a social media amma wasu lokaci after 4 hours sai inyi deleting dinshi, ba wai ina boye-boye bane ina kawai sabuwa ne irin tawa. Wata rana ma kunya nake ji. Ina wasa indai wasa ne kuma ina koyan amfanin social media sai dai yanzu hankali yana wajen yara na.
Wasu lokaci ma idan na fita da iyali na kan manta da waya na ma. kamar yanzu ma kun ganni na baro ta a mota ba.
An kwana biyu da jin wakar ki kwatsam sai kika fitar da wakar "Gbadu you"wanda kika yi da Tiwa Savage tare da shirin fitar da kunshin wakoki kwanan nan ya lamarin ya kasance haka?
Har yanzu ba fitar da EP din ba, wakar da nayi da yar uwa ta Tiwa kadai na fitar. Zamu fitar da wakoki nan bada dadewa ba don yanzu jiki ya dan yi karfi. kuma Ka san irin wannan abun ba kai kadai bane mai daukar mataki dole sai na tsara da mijina kuma gashi shima yana aiki nima ina aiki don haka abun ke daukan lokaci. Dalilin da yasa ban fitar da EP din kamar yadda ya kamata shine domin na san zan haihu. Na sake shi ne don a dandana.
Yanzu ma har mun fara yin bidiyo don haka kada ku damu akwai kayatattun wakoki da zamu fitar nan bada dadewa ba.
Zuwa yaushe kike sa ran zai fito?
Kada ka damu zaka sani. yanzu ma muna zagaye ne zuwa gidajen watsa labarai da yin wasa a wurare gabanin sakin wakokin. Ka sana mafi yawancin fans dina Underground ne su, wallahi baza ka gansu a ko ina amma idan ka hadu dasu zaka ji irin soyayyar da suke dashi a kaina. So ina son idan faran ta masu rai ta hanyar yin waka a wurare da dama lungu da tsako.
Wani irin sako kunshin wakokin zata isar wa al'umma?
A cikin EP din akwai wakoki bakwai, ka san in kana maganar lambar 7 is very Important. Nayi wakoki da yawa amma wadanan aka tantance.
A ciki akwai wakoki dake isar da labari na yau da kullum da muke fuskanta a cikin al'umma. Wakar 'Save me" tana bada labarin yadda al'umma suke nuna wariya da kuma kiran a kan yadda za'a gyara domin tabbatar da zaman lafiya. Bayan haka akwai wakoki na nishadi da kuma wadanda suke dauke da kida na tika rawa. Akwai na gantsarewa so duka dai muka hada a cikin ta. Na yishi bakwai ne don kowa ya samu wanda yake so.
Dawa dawa kika saka a cikin kunshin wakokin ?
Mutum biyu kawai suka fito a cikin ta. Reekado Banks da Tiwa savage.
Amma dukannin ku yan gida daya ne, babu yan waje?
A'a ba wai ba'ayi da mutanen waje. ana yi amma ka gane dalilin da yasa nayi haka shine a komai da zaka yi sai ka fara da gida kuma wannan shine first dina na fitar da kunshin wakoki. wannan ma har producers din ma yan gida ne.
A kullum muna cigaba da yima yan kasuwar Alaba godiya bisa yadda suke saka wakokin mu a ciki jarin wakoki da suke siyarwa a CD tare da gidajen rediyo da tibi. A Kaduna su DJs suna taimakawa, ku da kanku kuma kun san halaccin da kuke mana ai. Yanzu dai tunda nayi wanan daga wannan ai nishadantar da jama'a zan cigaba dayi.
Mutane na cewa kina dinki ya gaskiyan lamarin yake?
Ina son zane kaya ne bawai ni madinkiya ce. Wasu ne suka fitar da labarin cewa ina dinki. ai kowa na son fashion. Ga dauri nayi maku. Ni ko a harkar dinki T-shirt ne ma yake birge ni. Amma na kan yi ado in sa yan kunne ko kuma inyi daurin dankwali wanda ke daukan hankali. wata sa'i ma mahaifiya ta sai ta sani gaba sai nayi kwalliya.
Shekaru hudu kenan kina cikin Mavin, ya kika tsinci kanki cikin shekaru hudun a farfajiyar?
Tunda ina cikin ta har yanzu kai ma ka san ina jin dadi ko. Amma ka sam mai kamar yadda nake gaya ma kowa aikin nan namu ba yadda kuke kallon shi haka yake ba.Ba wai ka tashi da safe an baka komai da kake bukata. Kafin ma ka samu sauti mai dadi wanda zai mamaye kasa ai sai kayi akalla guda goma wanda daga ciki za'a tantance kana a zabi daya. Wata sa'i ma dogaro da Allah kawai ake yi idan an fitar da waka.
Wani abu da yasa nake son Mavin shine a dukkanin wakokin da kayi sai an zauna baki daya a tattauna kan wanda ake gani zai birge, ta hakan ma ake gani irin salon wakar da zai razanar da zukatan masu sauraro. Ni dai dalilin da har yanzu ban tsaya a bangare daya a fannin waka shine don ni ina yin waka ne a duk yanayin da ya tsinci kaina shiyasa zaka gan wata sai waka tayi dadi ko tayi slow ko tana dauke da kida da sauran su. Amma na san alot of music dina are very touching don a cikin EP dina m a nayi waka mai dauke da wanna yanayin. wanda ke sa mutum ya tambayi kansa game da wasu alamura na rayuwa.
Kin samu farin jini sosai musamman daga yan arewa, ya kika gan lamari shigowar ki Mavin kuma wani sako zaki ba masoyan ki na arewa?
Gaskiya yan arewa ina gode masu suna nuna mun kauna a ko da yaushe. kuma ALhamdulillah. Godiya nike yi kuma ina son ku dan cigaba da bani goyon baya don har yanzu a hanya nake ban kai ga masauki na ba. Bari kaji zamu yi alot a arewa wannan karon kasan mu dan zagaya wajen gida yanzu zamu dawo gida. Don haka kafin shekarar nan ta kare zamu yi abubuwa da dama a arewa. Next month ma za'a ganni a jihar Kano In sha Allah.
Ya kike dauki yanayin da kike ciki yanzu ganin kin zama mahaifiyar yara biyu kuma kina kokarin cinma manufar ki a waka?
Ka san irin wannan tambaya idan anyi mun sai ince ai ba ni na fara yin wannan ba don akwai wadanda suka fara gabani na dole nima na koya daga wajen su. Akwai mata masu yara guda bakwai amma suna cigaba harkokin su. Ni dai a gare ni akwai teamwork wato kowa na da hadin kai. Ina da iyalai da yan uwa dake zuwa suyi taimako, mijina ma yana taimakawa. Wata sa'i idan na fita mama na tana kula mun da yara ko yan uwanta. Ban da haka akwa su managers dina da ma'aikatan sa wadanda ke taimaka mun. duk wadanda muke aiki tare mun zama iyali ko wa na gida ne bana shakku ko fargaba idan suna nan.
Ta yaya mawakan arewa zasu samu cibiya wanda zai daukaka su duba da dinbim masu basira da ake dasu a yankin?
A duk halin da ka tsinci kanka sai ka gode ma Allah. Akwai artist da suka yi suna a nan Legas amma asali daga arewa aka far jin su. Ina gani idan aka fara daga gida zai taimaka.