Maaikatar  dake kula da harkokin jirgin sama ta bayyana cewa ana daf da fara kaddamar da jigilar mutane da jirgin kasa.

Ministan mai'aikatar, Hadi Sirika, ya bayyana cewa jirgin zata fara aiki cikin watan Disamba na wannan shekarar.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya amshi bakonci ma'aikatan hukumar lura da ka'idoji ta ICRC karkashin jagorancin shugabanta, Mista Chidi Izuwar.

Bayan takardar shaida da ma'aikatan hukumar suka mika masa na tabbatar da kaddamar da aiklin sufuri da jirgin sama, ministan yace takardar shaida ce na tabbatar da nisan aikin da suke yi.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana kaddamar da jiragen zata ci dala miliyan $8.8 gabanin aiwatarwa kana za'a kashe miliyan $300 a kan kula da harkokin jigila kafin riba su fara shigowa.

Sai dai batun farfado da kamfani jirgin saman na tare da hadin guiwan yan kasuwa, inda ministan ya ce ita ce hanyar da ta fi dacewa da za a dauki lokaci ana cin moriyarsa.

Ministan yace jiragen farko da zasu fara jigila zasu fara aiki ranar 19 ga watan Disamba na bana.

A shekarun baya kamfanin jirgin saman Air Nigeria tayi tasiri wajen jigilar jama'a zuwa jihohi da dama har ma da kasashen waje  sai dai kamfanin ta fuskanci kalubale wanda yayi sanadin mutuwar ta. Ana zargin mutuwar kamfanin kan dalidali dake da nasaba da rashin kulawa daga bangaren gwamnati da kuma sakacin ma'aikatan kamfanin.