Pulse.ng logo
Go

Malam Ibrahim Shekarau Gwamnati Buhari na tafiyar da mulki tamkar bata san abun da take yi ba - Inji tsohon gwamna

Ya kara da cewa gwamnatin bata aiwatar da wani aikin azo a gani ba kuma rawar da take takawa tamkar ayyukan yabo ba fallasa.

  • Published:
Shekarau tells PDP why he wants to become president play

Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau

(Royal Times)

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam'iyar adawa ta PDP yayi fashin baki game da mulkin shugaba Muhammadu Buhari a tsawon shekaru uku da yake saman kujerar.

Malam Ibrahim Shekarau yace gwamnatin Buhari tana gudanar da mulki tamkar bata san abun da take yi ba.

Tsohon gwamna wanda ke neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019, yayi wannan bayani ne a hirar da yayi da BBC hausa.

Shekarau wanda a baya yayi gwagwarmayar siyasa tare da goya bayan Shugaba Buhari yana mai cewa "Hatta wadanda suke adawa da gwamnatin sun yi mamakin yadda ta gaza wurin aiwatar da abubuwan da ta yi alkawari".

Ya kara da cewa gwamnatin bata aiwatar da wani aikin azo a gani ba kuma rawar da take takawa tamkar ayyukan yabo ba fallasa.

Tun ba yau ba ake cacar baki tsakani gwamnatin APC wanda ke samna kujerar mulki a halin yanzu da jam'iyar adawa ta PDP wanda ta mulki kasar tsawon shekaru 16.

Game da zarge-zarge da PDP take mata, APC tana mai daga kirji cewa ta farfado da tattalin arzikin kasa wanda jam'iyar adawa ta ruguza a tsawon shakarun da tayi a kujerar mulki.

APC ta kara da cewa ta sanya kasar kan hanyar dogaro da kai ba da hanyoyin samun kudaden shiga banda na man fetur.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.