Bayan shekara sha biyu yana gwagwarmaya wajen zama gwanin jamiya na takarar shugaban kasa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya cinma burin shi inda yayi nasarar zama gwanin babban jamiyar adawa ta PDP.

Atiku ya doke sauran yan takarar jam'iyar kama daga Rabiu Musa Kwankwso, Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal, Attahiru Bafarawa, Ibrahim Dankwambo, Datti Baba-Ahmed, David Mark, Tanimu Turaki, Jonah Jang, Ahmed Makarfi da Sule Lamido.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya samu nasarar ne bayan zaben fidda gwanin da PDP ta gudanar tare da karon kasa a garin Fatakwal babban birnin jihar Rivers wanda ya kama tun ranar Asabar 6 ga wata zuwa washe garin ranar Lahadi 7 ga wata.

Ya samu kuri'u mafi rinjaye cikin da 4,000 da aka kada.

Ga yadda sakamakon zaben ya fito;

Atiku Abubakar - 1532

Aminu Waziri Tambuwal -  693

Bukola Saraki - 317

Rabiu Musa Kwankwaso - 158

Ibrahim Dankwambo - 111

Sule Lamido – 96

 Ahmed Makarfi – 74

Tanimu Turaki – 62

David Mark – 32

Jonah Jang – 19

Datti Baba-Ahmed – 5

Kuri'u 68 aka soke a matsayin wadanda basu da amfani.