Pulse.ng logo
Go

Takardar difloma Gwamnatin tarayya ta sauke takardar HND na makarantun kimiya

Gwamnati ta sauya sunan makaratun kimiya dake jihar Legas da Kaduna. Makarantar Yaba college of technology zai koma City Univercity of Technology. Hakazalika Kaduna Polytechnic zai koma City University of Technology, Kaduna

  • Published:
KADPOLY suspends lecturer who collects money from students to let them cheat play

Kaduna Polytechnic Gate

(Inside Arewa)

Gwamnatin tarayya ta sauke bada takardun HND daga makarantun kimiya da fasaha dake fadin kasar.

Wannan matakin ya biyo bayan zaman majalisa da jami'an suka yi kamar yadda suka saba da shugaban kasa ranar laraba 6 ga watan Yuni a fadar shugaban.

Ministan ilimi Farfesa Adamu Adamu ya shaida wa manema labarai wannan matakin gabanin zaman da suka yi.

Ministan ya shaida ma yan jarida cewa "daga yau makarantu baza su cigaba da baga takardar HND ba".

Sai dai matakin zai fara aiki bayan dalibai dake karatu yanzu sun kammala karatun su na HND.

Wannan sabon mataki zai sanya makarantun kimiya su sauya wajen bada takardun digree a bangaren kimiya bayan kammala karatun ND. Bayan kammala karatun dalibai zasu samu takardar Bachelor of Technology (B.TECH)

Daurawa da wannan sabon matakin gwamnati ta sauke karatun darusan wadanda basu shafi  kimiya daga makaratun.

Bugu da kari gwamnati ta sauya sunan makaratun kimiya dake jihar Legas da Kaduna. Makarantar Yaba college of technology zai koma City University of Technology. Hakazalika Kaduna Polytechnic zai koma City University of Technology, Kaduna.

Bisa ga wannan sabon tsari, jami'o'a zasu dauki alhakin kula da makarantun kimiya kuma shugabannin jami'a zasu zabi wanda zai jagoranci makarantar.

Daga karshe dai ya bayyana cewa wannan matakin ba zai shafi wadanda suka kammala karatu da takardar HND inda ya kara da cewa zasu cigaba da amfani da takardar tamkar wanda ya kammala karatun digiri

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.