ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnatin tarayya ta bada ranakun hutu

Ministan yayi hakan ne a garin Abuja ranar litinin 11 ga wata a cikin wata takardar sanarwa da sakatare na din-din din na mai'aikatar sa ya sa hannu.

A wata sanarwa da ministan ayyukan cikin gida, Abdulrahman Dambazau yayi, an bada ranar juma'a 15 ga wata da ranar litinin 18 ga wata a matsayin ranakun hutun.

Ministan yayi ma dinbim mabiya addinin musulunciki farin ciki da kammala azumin watan ramadan, ya kuma yin kira na ayi amfanin da ranakun shagulgula wajen yi ma kasa addu'a na samu zaman lafiya, hadin kai da cigaba.

Yayi kira ga yan kasa da su cigaba da mara ma gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari domin cimma manufar kai kasar inda ya kamata.

Daga karshe dai yayi ma yan Nijeriya fatan barka da sallah.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT