Pulse.ng logo
Go

Azumi cikin walwala Gwamnatin jihar Jigawa ta karya farashin shinkafa ga ma'aikatan ta

Ta rabawa ma'aikatan jihar da shinkafa cikin farashi mai rahusa wanda zasu biya cikin wata biyu.

  • Published:
Yobe distributes 17,501 bags of rice, other items to IDPs, orphanages play

Yobe distributes 17,501 bags of rice, other items to IDPs, orphanages

(Facebook/rariya)

Gwamnatin jihar Jigawa ta karya farashin buhun shinkafa ga ma'aikatan jihar domin suyi azumin ramadan cikin walwala.

Ta rabawa ma'aikatan jihar da shinkafa cikin farashi mai rahusa wanda zasu biya cikin wata biyu.

kamar yadda majiya Rariya suka ruwaito, gwamnatin jihar ta bada wannan shinkafar ga ma'aikatan kananan hukumomin jihar kan farashin naira dubu goma sha biyu tsabanin dubu sha huda da ake siyarwa a kasuwa.

Gwamna Abubakar Badaru ya dauki wannan matakin ne domin taimakawa al' ummar jihar samun yin azumi cikin nishadi da walwala.

Ya kuma yi alkawarin biyan dukanin ma'aikatan jihar kudin hutun su cikin lokaci domin su samu su tafiyar da tsabgogin yau da kullum.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.