Pulse.ng logo
Go

Zaben fidda gwani Muhammadu Bindow ya samu tikitin sake tsayawa takara

Bindow ya doke kanin uwargidan shugaban kasa, Halilu Ahmed da kuma tsohon shugaban hukumar EFFC, Nuhu Ribadu, wajen zama gwanin APC a zaben 2019.

  • Published:
Gov. Bindow seeks blood donation for victims play Gwamnan jihar Adamawa Muhammed Jibrilla Bindow (Leadership)

Gwamnan jihar Adamawa, Muhammadu Jibrilla Bindow ya nasarar zama dan takarar gwamnan jam'iyar APC a jihar Adamawa.

Bindow ya doke kanin uwargidan shugaban kasa, Halilu Ahmed da kuma tsohon shugaban hukumar EFFC, Nuhu Ribadu, wajen zama dan takarar APC a zaben 2019.

Shugaban kwamitin zaben jihar Adamawa na jam'iyar, Ahmed Jibrin ya sanar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

Shugaban ya sanar da haka ne a safiyar ranar Lahadi 7 ga watan Oktoba inda yace gwamnan ya samu kuri'u 193,656 yayin da sauran abokan takarar sa suka samu 15,738  da  8,364.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement