ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamna Kashim Shettima yayi gani-kashe ni da littafai a Jamus

Hakan ya faru ne yayin da gwamnan ya tafi kasar Jamus domin halartar taro kan yankin tafkin chad.

Gwamna Kashim Shettima yayi tafiya zuwa kasar Jamus kana ya garzaya wani kantin sayar da littafai dake nan birnin Berlin.

A hotunan da suka mamaye shafukan dandalin sada zumunta an gan inda gwamnan ya dukufa a kantin yana neman littaafi ba tare da yayi la'akari da matsayin shi.

Hotunan dai sun jawo cece-kuce inda wasu ke ganin cewa tun asali gwamnan yana ta'amali da littafi domin fadada ilimin sa hakazalika wasu na da ra'ayin cewa gwamnan ya nuna ma duniya cewa duk da halin da jihar sa Borno ke cike sakamakon aika-aikar mayakan Boko haram al'ummar jihar na alfahari da neman ilimi.

ADVERTISEMENT

Gwamnan ya kai ziyara birnin Berlin ranar takata ne inda ya halarci taro kan  yankin tafkin Chad.

Sakamakon taron an tallafa ma yankin da kudi dala biliyan 2.17 ($2.17bn).

Kamar yadda jakadan Nijeriya zuwa kasar Jamus Ambasada Yusuf Tuggar ya sanar a shafin sa na Twitter, an bada tallafin ne domin samad da ayukan cigaba a yankin.

Nijeriya, Jamus, Norway da majalisar dinkin duniya suka jagorancin taron kan batun yankin tafkin chad.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT