Daya daga cikin matakin da ya dace wajen yawaita aikin ibada a cikin ranakun nan domin yin dace da daren Laylatul Qadr shine kebancewa a masallaci ta hanyar itikafi.
Hanyoyi 10 da zasu taimaka wajen cinma manufar yin Itikafi
Idan kuna tunani kebancewa a dakin Allah domin yin ibada a cikin goman karshen wannan wata mai albarka ta hanyar itikafi, ga wasu abubuwa 10 da zai taimaka wajen cinma wannan manufar.
Zaka iya inganta ibadun ka yayin yin itikafi idan ka bi wadannan sharuda
1. Tsarkake niya
Ka tabbatar cewa zaka shiga itikafi ne domin ibada tare da inganta imanin ka. Mutum yayi la'akari da hadisin farko na littafin "hadisai 40" na imam nawawi.
2. Ka tsara tare da kula da ayyukan ibada da zaka yi yayin da ka shiga itikaf
Wannan zai taimaka wajen daura ka a kan hanya kuma ya inganta niyyar da ka dauka na yin aikin. Daya daga cikin abubuwa da yin haka zai yi ma shine kula da adadin ayoyin da ka karanta ko kuma yawan zikirin da kayi bayan ka kayyade wanda zaka yi.
3. Ka zamanto mai yawaita karatun al-qur'an a ko wani lokaci
Hakika a cikin wannan watan Allah madaukakin sarki ya saukar da Al-Qur'ani, yi amfanin da wannan damar wajen yawaita karatunta domin samun ladar dake cikin yin haka. Ka sani cewa ko wani harafi da ka karanta a cikin wannan wata yana da lada 700 ko fiye da haka.
4. Ka yawaita nafilfili
Daya daga cikion ayyukan da zai taimake ka wajen sadu da mahalli ka shine ta hanyar yawaita yin nafilfili.
5. Haka zalika ka yawaita yin zikiri
Harshen ka shima ya kasance mai tunawa da Allah ta hanyar yawaita zikiri
6. Ka dukafa wajen yin addu'o'i tare da neman gafarar Allah
Yayin da ka shiga aikin Itikafi, ka sani cewa lokaci ne da zaka yi addu'a ma kanka da sauran yan uwa har ma da sauran al'ummar musulmai na fadin duniya.
7. Ka kauarace yin maganganu mara riba ko wanda ya saba wa manufar shiga itikaf
Ka kaurace wajen yin magannun siyasa, wasanni, labarin Nishadi da makamantar su. Yayin da ka shiga Itikafi ka kaurace ma labarun duniya ka dukufa wajen yawaita yin ibada
8. Ka takaita yawan cin abinci da yin bacci
Itikafi ba lokaci bane wanda ake baje kolin cin abinci ko yawaita yin bacci. Idan ka shiga masallacin da niyar yin Itikafi ka sani cewa ka shigane don yin ibada ba don ka kaurace ma wahalhalun da kake fuskanta ko neman hutu daga aikin da kake yi na yau da kullum.
9. Kada ka fita daga masallaci sai dai idan ya zama dole
Wasu daga cikin abubuwan da zasu sa mutum ya fita daga masallaci sune;
Domin alwala, yin tsarki ko yin wanka.
10. Ka yawaita ibada domin yin dace da daren laylatul qadr
Daren Laylatul Qadr ta bambanta da sauran dararraki domin kuwa Allah (SWT) ya bada falalar dake cikin ta a cikin Littafi mai girma.
Dare ne wanda ya yafi watanni 1000 albarka. Ana iya yin dace da ita a goman karshen nan.
Kayi amfani da wannan damar wajen yawaita ibada domin yin dace da wannan daren mai dinbim falala.
Kamar yadda aka ruwaito a hadisin manzon Allah, musulmi ya yawaita yin wannan addua domin yin dace da Laylatul Qadr “Allahumma innaka ‘afuwwun tuhibbul ‘afwa fa’fu ‘annee.
Muna fatan Allah yasa mu dace da wannan daren kuma ya amshi ibadun
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng