Pulse.ng logo
Go

Labari cikin hotuna Gawar Khalifa Isyaka Rabiu ya sauka jihar Kano daga birnin London

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar gwamnatin sa wajen taren gawar yayin da ta sauka a safiyar yau.

  • Published:
Gawar Khalifa Isyaka Rabiu y sauka Kano play

Gawar Khalifa Isyaka Rabiu y sauka Kano

(Twitter/SalymBabajo)

Gawar fitaccen malami kuma hamshakin dan kasuwa, Khalifa Isyaka Rabiu ya sauka filin jirgin saman Aminu Kano.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar gwamnatin sa wajen taren gawar yayin da ta sauka a safiyar yau.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sauran tawagar gwamnatin sa wajen tare gawar play

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sauran tawagar gwamnatin sa wajen tare gawar

(Twitter/SalymBabajo)

 

kamar yadda iyalen sa suka sanar, za'ayi jana'izar shi bayan sallar juma'a a masallacin sa dake goron dutse.

 

Marigayin ya rasu a asibiti dake birnin London yammacin ranar talata 8 ga watan mayu, bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Gwamnatin jihar Kano, a cikin wata takarda da kwamishnan labarai, Mallam Muhammed Garba ya fitar, ta kaddamar da ranar Juma'a a matsayin ranar hutu domin ma'aikatan jihar su samu damar halartar jana'izar tare da mika ta'aziya ga iyalan sa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.