Ga yadda senegal ta fita gasar bana duk da cewa ta hada maki da na biyu a rukunin ta

An kafa tarihi a gasar wannan shekarar sakamakon fitar kasar yammacin nahiyar Afrika bayan wasan ta da Kolombiya.

Hakan dai bai taba samuwa ba a tarihin gasar tun bayan na shekarar 1982.

Wasan ta na karshe na rukuni da Kolombiya, Senegal na bukatar yin kunnen doki ko ta samu galaba domin tsallakewa zuwa zagaye na biyu. Sai dai hakan bai faru ba inda a cikin minti 77 na wasa mai tsaron bayan Kolombiya, Yary Mina, ya zura kwallo a ragar mai tsaron gidan Senegal wanda yayi sanadiyar rashin tsallakewar su.

Senegal ta hada maki daya da Japan wanda da ita za'a tantance kasar da zata tsallake zuwa zagaye na biyu. Japan ta samu galaba kan SEnegal na ketara kasancewa kasar Afrika ta fita samun kati a wasannin da ta buga.

Matakin yana daga cikin ka'idoji da hukumar kwallon kafa na duniya ta kafa a gasar.

Mai horas da yan wasan Senegal, Aliou Cisse, yace ya rungumi kaddarar da ya fada a kan su. A cewar sa babu wata mafita dangane da lamarin domin ka'ida ne wanda FIFA ta kafa kuma kowa ya amince dashi.

"Dokar kwallo ne. Bamu yi nasarar tsallakewa ba domin mun fi samun kati fiye da abokan takarar mu amma, ina alfahari da yan wasan mu. Sun nuna bajinta a gasar bana kuma ina ganin mun nuna ma duniya cewa zamu birge jama'a nan gaba" yace.

Rashin nasara kasar ya jawo bakin ciki a zukatan yan afrika masoya kwallo kafa. Da dama sun bayyana bacin ran su kan sakamakon wasan Senegal da yadda dokar FIFA ta fitar da ita.

Gasar bana dai shine na farko bayan shekaru 36 da kasar Afrika bata samu nasara na tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

These 6 countries have the highest unemployment rates in Africa

These 6 countries have the highest unemployment rates in Africa

Top 10 happiest countries in Africa in 2022

Top 10 happiest countries in Africa in 2022

'Funke and my dad cheated on each other' - Funke Akindele's stepson continues to drag her on Instagram

'Funke and my dad cheated on each other' - Funke Akindele's stepson continues to drag her on Instagram

Here are the top 10 African countries that smoke the most cannabis

Here are the top 10 African countries that smoke the most cannabis

9 most expensive African countries to rent a one bedroom apartment, based on property price to income ratio

9 most expensive African countries to rent a one bedroom apartment, based on property price to income ratio

Blossom Chukwujekwu's ex-wife Maureen Esisi reacts as he remarries

Blossom Chukwujekwu's ex-wife Maureen Esisi reacts as he remarries

Quiz: Only genuine Nollywood fans will score 8/8 on this Blood Sisters quiz

Quiz: Only genuine Nollywood fans will score 8/8 on this "Blood Sisters" quiz

Here are the top 10 cities in Africa where the most rich people live

Here are the top 10 cities in Africa where the most rich people live

Lagos NURTW Caretaker Chairman accuses MC Oluomo of snatching his wife

Lagos NURTW Caretaker Chairman accuses MC Oluomo of snatching his wife