Bakin ciki da hawaye ya mamaye zukatan tawagar yan wasan kasar ingila da magoyan ta sakamakon galabar da Croatia ta samu wasan su na daf da karshe a gasar cin kofin duniya.

Sakamakon wasan wanda aka buga ranar laraba 11 ga wata a filin Luzhniki, Croatia tayi nasarar ketarawa zuwa wasan karshe na gasar bana, ta doke Ingila da ci 2-1.

Wannan shine karo na farko da kasar mai yawan jama'a kimanin miliyan 4.4 zata kai wasan karshe a tarihin gasar duniya.

Duk da cewa Ingila ta fara zura kwallo a wasan, tawagar yan wasan Croatia sun rama cin da Ingila tayi tare da daura wani bayan karin lokaci da aka bayan kammala minti 90 da kunnen doki.

Dan bayan , Kieran Trippier, ya zura ma tawagar Ingila kwallo a raga cikin minti 5 da fara wasa. Sakamakon ya tsaya hakan har karshen wa'adi na farko.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci Perisic ya rama cin da Ingila tayi ma Croatia. Lamarin wasan ya tsaya hakan har karshen minti 90 na wasan.

Cikin mintin Extra time dan wasan gaban Croatia, Mario Mandzukic ya katse gudun Ingila a tseren wa zai kai wasan karshen gasar.

Ingila ta nemi ta sake daukar kofin duniya bayan tsawon shekara 52 da daga ta.

A wasan karshe na gasar bana Croatia zata nemi ta haye Faransa ranar Lahadi 15 ga watan Yuli domin daga kofi.

Ingila zata nemi zama ta uku a gasar wasan ta da Belgium ranar asabar.