Rigar dai ya birge ganin yadda aka yi mata ado da tambarin mikiya da irin launin tutar Nijeriya.
Tawagar super eagles sun garzaya Rasha sanye da rigar gargajiya
Yan wasan sun garzaya kasar ne inda zasu gwabza da sauran kasashen duniya a gasar cin kofin duniya wanda za' a fara ranar alhamis 14 ga wata.
Gabanin tafitar tasu, tawagar ta yada zango kasar Austria inda suka motsa jiki domin shirya ma gasar.
Super eagles tana rukuni daya da kasar Croatia da Iceland da Argentina kana wasan su na farko zasu kara da Croatia ranar 16 ga wata.
Cikin shirye-shirye da suka yi ma gasar, Nijeriya ta buga wasannin sada zumunci da kasar DR Congo da Ingila da Czech Republic.
A dukannin wasanin da ta buga, bata yi nasarar lashe ko wasa daya ba. Tayi kunnen doki da Congo inda ta tashi 2-1 wasan ta da Birtaniya daga nan kuma Czech tayi nasara da 1-0 wasan a kasar Austria.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng