Labari ya bayyana cewa shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Al-garkawi wanda masu garkuwa da mutane suka sace ya koma ga iyalen.

Malamin yua koma gida bayan kwanan uku a hannun barayin.

A rahoton da jaridar Premium times ta fitar, kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya tabbatar da sakin malamin.

Ya kara da cewa suna bincike kan wasu mutane biyu da aka kama da zargin sa hannunj su wajen sace shehin malamin.

Barayin dai sun sace malamin ne a yammacin ranar alhamis a gonar shi dake wajen garin Kaduna tare da wasu daliban sa su uku.

Sai dai yan sanda basu yi karin haske game da daliban sa da aka sace tare dashi.