Kwamitin sun samu cêwa án kulle kujeri da tabûr a wani makaranta wanda ɗalibai ke zama ƙasa
An gane wannan a lokacin da an kai kima a makarantar sekandare mai suna Hafsatu Ahmadu Bello, Sokoto.
Da yáke báyar da kalamai, wakilin Gwamnan Sakkwato-Imam Imam, ya cê an gane wannan a lokacin da aka kai kima a makarantar sekandare na Hafsatu Bello, Sakkwato. Ya ce:
"Ƴan ajuju ƙadan suke da kujeran zama. Tun da daɗewa, ɗálibai sun yi hanƙuri da zama a kan ƙasa kawai.
"Yawancinsu na karatu da kuma ƙarban lacca akan tabarma domin kare fararen kaya daga ƙura ko ƙasa, kuma wasu suna zuwa da zâni domin shimfidawa akan ƙasa.
"A yayin da suke fama da wannan hâlì mai rashin daɗi, an kulle tebur da kujeri a cikin wasu ajujuwa nan kusa da ajinsu, an bari waɗanan teburi da kujeri su fara lalacewa da ruɓewa".
Muna da labari cewa ɗaliban wannan makaranta, sun kai ƙarshe na shan wuya a makon, bayan kwamiti sun kai kima ga wurare da dama cikin makaranta domin yin shawarwari game da maganin waɗanan matsalolin da aka gano.
A cikin kalamai, an ƙara bayani cewa shugaban tawagar, Likita Shadi Sabeh, ya umurce shuwagabanin makaranta, su raba kujeri da teburi ga kowane aji a nan take.
Ya umurce shuwagabanin makaranta su mayar da hankali su ga biyan buƙata da kuma kulá da ɗalibai.
An yi umurni cêwa, daga lokacin, haɗin kai da gwanati domin gyaran makarantu, ya zama wajibi ga masu kula da makaranta. Wannan shine domin kada a yi zarginsu da ɓarnan ayyukan Gwamnati da gangan.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng