Bayan sama da mako hudu da sace yan matan, mayakan sun dawo dasu daidai garin da suka sace su.
Gargadin da yan boko haram suka yi yayin da suka saki daliban Dapchi
Kamar yadda jaridar Associate press ta bayyana, yan ta'adar sun ja kunnen al'ummar garin kan hana yan matan komawa makaranta
Kamar yadda jaridar Associate press ta bayyana, yan ta'adar sun ja kunnen al'ummar garin kan hana yan matan komawa makaranta.
Wani shaidar gani da ido mai suna Mohammed Ali ya bayyana ma manema labaran NAN cewa yan ta'addar sun bayar da shawara na a aurar dasu.
Yana mai cewa " Su da kansu suka mayar da yan matan. sai da ma na gaisa da wasu gud biyu daga cikin su. matasa ne masu kwazo sai dai suna tare da makamai. Sun yi mana gargadi na kada mu bari yan matan su koma makaranta. Shawarar da suka bayar shine na a yi masu aure."
Yawon yan matan da aka saki
Kan batun dawowar su gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kididdigin da aka gudanar ya tabbatar cewa yan matan su 104 a dawo dasu tare da wani yaro.
Sai dai har yanzu akwai sauran mace daya daga cikin yan matan a hannun mayakan kuma dalibai biyar sun rasu daga cikin yan mata 110 da aka sace.
kamar yadda daya daga cikin yan matan da aka saki ta bayyana, an cigaba da rike daya daga cikin su domin taki amincewa ta sauya addinin zuwa musulunci.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng