ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ga martanin da wasu yan kasa suka mayar game da furucin Shugaban kasa

Kalaman nasa ya tayar da kura inda jama'a da dama suka nuna facin ran su a kafafen sada zumunta

A taron shugabanin kasashen rainon Ingila wanda aka gudanar a Londan makon da ya gabata, shugaban kasa  Muhammadu Buhari yayi wasu kalaman wanda ya tayar da hankulan yan Nijeriya musamman matasan kasar.

Shugaban yana mai cewa mafi yawancin matasan Nijeriya cima-zaune ne masu neman samun komai cikin sauki tare da yin takama da arzikin mai.

Kalaman nasa ya tayar da kura inda jama'a da dama suka nuna facin ran su a kafafen sada zumunta.

Ga wasu daga cikin martanin da wasu suka yi;

ADVERTISEMENT

*

Gani wani sako da wani ya sakar kuma kan lamarin

Martanin fadar shugaban kasa

Sai dai fadar shugaban kasa ta mayar da martani inda ta sanar cewa anyi ma kalaman shugaban mummunar fahimta.

Kan wannan batun wanda ya tayar da kura kuma ya zama abun muhawara a fadin Nijeriya, mukarraban shugaban sun mayar da martani.

ADVERTISEMENT

Hirar shi da gidan telebijin na Channels, kakakin shugaban, Femi Adeshina yace yan Nijeriya sunyi ma shugaban mummunar fahimta domin ba duka matasan ya hada wajen yi masu kudin goro ba.

A cewar sa wasu makiyan shugaban suka yi amfani da wannan damar wajen ruruta furucin sa wanda suka yi ma fahimtar iska domin watsa ma shugaban kasa a ido.

Haka zalika shima mai bai wa shugaban shawara kan kafafen watsa labarai, Sha'aban Sharada ya kara da cewa matasan basu fahimci kalaman shugaba Buhari.

Yace "Duk wanda ya kalli bidiyon Shugaba Muhammadu Buhari zai ga cewa ya furta kalaman ne cikin raha".

Ya ce furucin da shugaba Buhari ya yi hannunka mai sanda ne ga al'ummar kasar domin su tashi tsaye wajen neman na kansu.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa a ko wanne lokaci batun yadda za a inganta rayuwar matasa shi ne babban abun da Shugaba Buhari ya sa a gaba.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT