Pulse.ng logo
Go

A jihar Jigawa Fusatattun mazaunin garin Dutse sun lakadawa shugaban karamar hukuma duka

Jama'ar garin suna zargin sa kan rashin biyan kudin asusun mazabar da ya kamata a biya su.

  • Published:
Dutse residents beat, imprison LG chairman over money play Fusatattun jama'ar sun kewaye ofishin karamar hukumar tare da hana shugaban fita daga cikinta (Premium Times)

Fusatattun jama'ar gari sun bayyana haushin su ga shugaban karamar hukumar Dutse, Bala Yargaba inda suka lakada masa duka tare da yin garkuwa dashi.

Jama'ar garin suna zargin sa kan rashin biyan kudin asusun mazabar da ya kamata a biya su.

Kamar yadda jaridar Premiumtimes ta ruwaito, lamarin ya faru ne a garin Dutse safiyar ranar litinin 9 ga watan Yuli.

Daruruwan mazaunin garin sun lasa ma shugaban duka wanda daga bisani yayi nasara kubucewa inda ya shiga harabar ofishin karamar hukuma.

Duk da aka basu saduda ba inda suka kewaye harabar ofishin tareda hana shugaban barin ofishin.

Labari ya nuna cewa jami'an rundunar yan sanda da sojoji sun garzaya ofishin domin kwato shugaban tare da kwantar da tarzomar da ya faru.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement