Tawagar yan wasan kwallon kafa ta kasar Spain ta kori kocinta bayan rashin nasara da suka samu a gasar kofin duniya na bana.

Fernando Hierro wanda ya maye gurbin tsohon kociyar tawagar, Jullen Lopetegui, wanda aka kora daf da fara gasar wannan shekarar sakamakon rashin jituwa da ya faru tsakanin sa da hukumar kwallon kafa ta kasar.

Tawagar ta raba gari da Lopetegui bayan sanarwa da kungiyar Real Madrid tayi na cewa shine sabon kocin da zai horasa da yan wasan ta. Hukumar ta dauki matakin korar shi bisa ga dalilin rashin sanar dasu da kocin yayi game da yarjejeniya da yayi da kungiyar.

Sanarwar ya fito ne ranar lahadi 8 ga watan Yuli.

Tsohon dan wasan Real madrid, ya cigaba da jagorantar yan wasan tawagar a gasar kofin duniya wanda tawagar ta fadi a zagaye na biyu wasan ta na kasar Rasha.

Rashin nasarar tawagar bai yi ma jama'a da dama dadi ba domin kyautata zaton da ake yi na cewa zata yi nasara na kaiwa zagaye na karshe ko kuma ta dauki kofin bana.

Bayan faduwar su, shima shahararren dan wasan ta kuma tsohon jagoran yan wasan Barcelona, Andres Iniesta, yayi murabus da taka leda da tawagar.