Pulse.ng logo
Go

Femi Falana Lauya yace zai kai karar gwamnatin tarayya kotu kan raunin da yaji sanadiyar hatsarin da ya samu

Yace sai ya kai karar gwamnati ga kotu ranar laraba kan ciwon da yaji sanadiyar hatsari

  • Published:
'We won't let FG violate your rights', Falana tells Obasanjo play

Human rights lawyer, Femi Falana

(File)

Sanannen alkali wanda ke yaki kan kare hakkin mutane Femi Falana (SAN) ya bayyana abun dake zuciyar sa na kai karar gwamnatin taraya kotu bisa ga lalacewa hanya wanda tayi sanadiyar hatsari da yayi inda ya saumu rauni.

Alkalin yace ya samu hatsarin ne a hanyar shi zuwa wajen aikin sa nan garin Abuja wanda yasa har aka kwantar dashi a asibiti domin ya samu karaya a kafar shi kana yace ba zai yi shuru ba game da batun kamar yanda sauran yan kasar keyi idan haka ya faru dasu.

Shi dai wannan babban alkalin Yace sai ya kai karar gwamnati ga kotu ranar laraba kan ciwon da yaji sanadiyar hatsarin.

Ya fadi haka ne a wani taro ta musamman da aka gabatar a garin Abuja ranar talata 14 ga watan Nuwamba.

Kwannan baya dai falana ya soke karar rundunar sojoji ga kwamitin bincike akan saba hakkin dan adam da shugaban kasa ya kafa game da sabawa doka wajen tsare shugaban yan darikar Shi'a Ibrahim Al-zakzaky fiye da yadda ya kamata.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement