ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnan yace tsohon gwamnonin jihar Kayode Fayemi da Segun Oni ba zasu iya lashe zaben 2018

Wannan labarin ya fito bayan sanarwan tsohon gwamnoni Kayode fayemi da Segun Oni na yin takara a zaben 2018

Governor Ayo Fayose

Yayi wannan sanarwan yayin da yake ganawa da jiga-jigan yan siyasa a gidan gwamnati na jihar Ekiti ranar juma’a 16 ga watan yuni 2017.

Fayose yace “ wasu sun dauka don Ayo Fayose yaci zaben karo na biyu don zama gwamna suma sun dauka suna iya dawowa, su sani wannan ba zai yiwu ba.”

“Nine wadda mutanen jihar Ekiti suka fi so don ayyukan raya ci gaban jihar da na kawo masu. In ka shiga ko wani lungu da sako zaka gan aikin da na kaddamar. Shiyasa  na zama jagoran mutanen Ekiti a zaben 2018.”

ADVERTISEMENT

“Kafin zaben 2018 zaku gan bambanci tsakanin mu da yan adawa. Ni tamkar uba ne a gare su. su ma sun sani. Naji wasu tsohon gwamnoni na neman dowowa don Fayose ya dawo. Babu laifi idan zasu gwada amma dai su sani ba zasu ci nasara ba.”

Gwamna Ayo fayose ya kara da cewa zai kayar da shugaba buhari a zaben 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT