ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamna Ayo Fayose yayi barazanar tona asirin Buhari

Fayose ya kara da cewa, uwar gidan shugaban kasa bata samu damar ganin mijinta ba lokacin da ta kai ziyara Landan

Governor Ayo Fayose

Fayose yayi barazanar fadi ma yan najeriya halin da shugaban kasa ke ciki a Landan inda yake neman magani.

Jaridar punch sun rubuto cewa, Fayose yace ciwon shugaban kasan yayi tsanani tun 6 ga watan Yuni 2017.

Gwamnan jihar Ekiti yayi kira ga tawagar Buhari dake yada labarai da su bayyana ma yan najeriya gaskiyar labarin ciwon shi, ya kara da cewa sakon murya da suka saki ranar sallah bogi ne.

ya kara da cewa, uwargida Aisha Buhari bata samu damar ganin mijinta lokacin da ta kai ziyara birnin landan.

ADVERTISEMENT

A bakin gwamnan; “ kwanan 53 kenan da shugaban kasar mu ya bar kasar don neman magani a kasar waje. Babu wani labari na  halin da yake ciki.”

“Kamar sauran yan kasar, ba wai ina fata shugaban kasa ya mutu. Nayi shuru kuma na dai san wannan shine karo na biyu da shugaba ke tafiya kasar waje don neman magani cikin wannan shekara”

“Sakon murya da aka saki ya janyo wannan maganar da nike yi. Shugaba yana da matsala wajen yanda yake magana”

“Wasu mutum 3 kadai dake boye ke da damar ganin shugaban kasa a halin yanzu. Ba zan fadi sunan su ba”

“Duk wanda ke ganin ba haka bane bisa ga abun da na fadi, toh ya fito mana da shugaban kasar najeriya kafin sa’o’i 48”

ADVERTISEMENT

A kwanan baya gwamna Ayo Fayose yayi shelar aniyarsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT