ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Fasto ya bada tallafin N1m wajen gina masallaci

Limamin cocin yace ya bada tallafin ne domin a samu a kammala gina babban masallacin da cibiyar adinin musulunci a jihar Cross Rivers

Babban limamin cocin Penial Church of God, Fasto Essien Ayi, yayi hakan ne domin taimakawa al' ummar musulmai dake nan jihar.

Ba bada tallafin ranar laraba 20 ga watan Yuni a dai dai unguwar Gbogobiri dake nan Calabar inda akasarin mazaunan yankin yan arewa ne.

Limamin cocin yace ya bada gudnmawar ne domin a samu a kammala gina babban masallacin da cibiyar adinin musulunci a jihar Cross Rivers.

Dan kabilar Yayi kira ga sauran jama da su zama masu taimakawa juna ba tare da nuna wariya ta hanya addini ko al'ada.

ADVERTISEMENT

A cewar shi duk wani addini dake akwai a duniya tayi imani cewa akwai Allah mahallicin komai. Don haka yayi hakan ne don cinma wannan manufar.

Fasto wanda aka zaba a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin  Akpabuyo/Bakassi/Calabar na jihar, yace tun ba yau ba al'umar hausawa dake garin suke mara masa baya. Yace tun yana rike da matsayin shugaban karamar hukuma suke goyon bayan sa kuma da suka tunkare shi game da aikin masallaci da suke bai yi jinkiri ba wajen tallafa masu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT