Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar wanda ya sauka daga mukamin sa kwanan baya ya sauya zuwa jamiyar PDP.

Tsohon mataimakin gwamnan ya yanke shawarar yin murabus daga kujerar shi bayan rashin jituwa da ya samu da gwaman jihar.

Babban na hannun daman tsohon gwamnan jihar sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma  jam'iyar da uban gidan sa yake ranar talata 7 ga watan Agusta.

Hirar shi da manema labarai bayan taron bikin komawar sa PDP, Farfesa Hafiz yace ya zama dole ya bar jam'iyar APC saboda irin azabtarwa da ya sha a cikin ta cikin yan shekaru da suka gabata.

Yace hakika zai samu sukuni a cikin sabuwar jam'iyar da ya koma tare da jaddada cewa har yanzu biyayyan da yake ma Kwankwaso tana nan kuma zai cigaba da goyon bayan sa a harkar siyasa.

Yayin da aka tambaye shi ko zai fito takarar kujerar gwamna na jihar, tsohon mataimakin yace zai sanar da jama'a idan lokacin yin haka yayi.

Martanin gwamnatin jihar Kano

A wata sakon sanarwa da kwamishnan watsa labarai na jihar ya fitar wa manema labarai, gwamnatin Kano ta mayar da martani game da komawar tsohon mataimakin jam'iyar adawa.

Sakon wanda kwamishnan Muhammed Garba ya sa hannu ya nuna cewa lamarin ba sabon labari bane domin tuntuni ake tunanin haka.

Sanarwar ta bayyana cewa tun da dadewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke sa ran zai dauki wannan matakin.