Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Farfesa Hafiz Abubakar, ya fice daga jamiyar adawa ta PDP zuwa PRP.

Farfesa Hafiz wanda ya sauka daga kujerar sa na gwamnatin Abdullahi Ganduje cikin watan Agusta ya bi sahun Kwankwaso na koma PDP.

Bayan watanni kalilan a cikin jam'iyar tsohon mataimakin gwamnan ya fice zuwa jam'iyar PRP bisa ga rashin adalci da aka nuna mashi tare da magoya bayan sa.

Yace ba'a shawarce shi ba game da wanda zai mara ma dan takarar gwamna na jihar Kano karkashin PDP.

Farfesa Hafiz ya kara da cewa tsohon jam'iyar sa bata amince da yunkurin da ya nema na baiwa dan takarar sa tikitin tsayawa takarar kujerar majalisar jiha.

Hafiz Abubakar ya sauka daga mukamin sa

Tsohon mataimakin gwamnan ya yanke shawarar yin murabus daga kujerar shi bayan rashin jituwa da ya samu da gwaman jihar sakamakon komawar Kwankwaso jam'iyar PDP.

Gabanin mika takardar ajiye aikin da yayi, tsohon mataimakin gwamnan ya shaida wa BBC cewa shi da gwamnan suna zaman doya da manja saboda yana tare da tafiyar Kwankwasiya kuma lamarin ta kai ga yi ma raywarsa barazana.