Shugaba Muhammadu Buhari yayi ido hudu da fom din tsayawa takara da aka siya mashi a kan N45M.

Kungiyar Nigerian Consolidation Ambassadors Network  karkashin jagorancin shugaban ta Alhaji Sanusi Musa ta mika ma shugaban fom din a fadar sa ranar Talata 11 ga watan Satumba.

A ranar 5 ga wata kungiyar ta siya takardar tsayawa takarar shugaban domin ya zarce da mulkin kasa bayan sun nuna gamsuwar su ga shugabancin sa.

A jawabin sa yayin da ya karbin tawagar kungiyar, shugaba Buhari yayi masu godiya bisa yarda da suka yi masa.

Jim kadan bayan jam'iyar APC ta fitar da kudaden neman takarar ta gabatar da kudin neman takarar shugaban.

Ta mika takardar miliyan arba'in da biyar ga shugaban jam'iyar Adams Oshiomole.

Sanusi ya shaida cewa ya'yan kungiyar tunda daga karkara da kananan hukumomi na jihohin kasa suka hada kudin siyan takardar domin nuna gamsuwar su ga shugabancin shugaba Buhari.