Hukumar jamian fararen hula ta DSS ta samu sabon jagora bayan am sallami tsohon shugaban ta Lawal Daura sakamakon lamarin da ya faru a harabar majalisar dokoki.

Dan jihar Bayelsa Mathew Seiyefa shine wanda ya maye kujerar korarren tsohon shugaban kasancewa shine jami'i mai matsayi mafi girma a hukumar.

Tsohon shugaban ya fuskanci sallama ne sakamakon kawanya da wasu jami'an rundunar DSS suka yi ma zauren majalisar tarayya inda suka hana shiga da fita.

Jim kadan bayan faruwar lamarin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sanar da matakin sallamar shugaban rundunar.

A rahoton da tashar telibijin na Channels tv ta fitar, shugaban kasa mai riko ya kuma gana da sabon shugaban hukumar tare da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.