ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari ya baiwa hukumar EFCC da ICPC damar cafke Babachir da Oke

Shugaban ya sha alwashin hukunta duk wanda ke neman gurbata anniyar shi na ƙawar da cin hanci da rashawa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa hukumar EFCC da ICPC damar tuhumar tsohon sakataren gwamnati ƙasa da tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA wanda ya kora.

Buhari ya sallame jami'an gwamnatin jiya 30 ga watan octoba bisa ga rahoton da kwamiti dake bincike akan su wanda ya kafa suka kawo.

Ana zargin su da aikata laifin da ya danganci cin hanci da rashawa.

Da haka shugaban ya baiwa hukumar hana zamba ta EFCC da ICPC damar cigaba da bincike akan Babachir Lawal da Ayo Oke.

ADVERTISEMENT

A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa Garba Shehu yayi a daren ranar litinin, shugaban ya sha alwashin hukunta duk wanda ke neman gurbata anniyar sa na ƙawar da cin hanci da rashawa.

Sanarwan ya fito bisa ga cece-kuce da yan ƙasa keyi na neman sanin hukunci da shugaban zai dauka bayan ya sallami jami'an.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT