Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi kiran jan kunnen ga shugaban ma'aikata Abbah Kyari tare da shugaban hukumar ma'aikata na tarayya Winifred Oyo-ita.
Buhari ya ja kunnen yan majalisar sa dake neman tada kura yayin da ake zaman majalisa
Rahotanni na nuna cewa jami'an sun samu sabanni bisa ga lamarin komawar Abdurasheed Maina aiki
Wannan ya fito ne bayan jami'an sun nemi su kece raini sanadiyar saɓani da suka samu a zaman majalisar zartarwa ranar laraba 1 ga watan Nuwamba.
A bisa labarin da jaridar Punch ta fitar, ana zargin cewa jami'an sun samu saɓani bisa ga lamarin komawar Abdurasheed Maina aiki wanda ke tada kura a kasar.
Majiyar mu yace Kyari yana zargin Oyo-ita da sakin wasikar da ta turo mai ga jama'a wanda bai kamata tayi hakan ba.
Majiyar yace shugaban bai da dadi ganin abun da ya faru tsakanin jami'an sa kuma ya bada umarni na su ganshi nan take bayan an gama zaman majalisar.
Wannan abun kunya ya faru a bainar sauran yan majalisar a zaman da suke ko wani mako a faɗar shugaban kasa na Villa.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng