Pulse.ng logo
Go

El-rufai Gwamna yana neman taimakon jama’a wajen shawo kan almajiranci

Gwamnan yayi wannan rokon a wani taron wayar da kai akan illar bara da sakomakon ta wajen tabbatar da tsaro a kasa ranar talata

  • Published:
Gwamnan jihar Kaduna play

Gwamnan jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Mallam nasir El-rufai ya bayyanar cewa dole a nemi taimakon al’ummar jihar wajen kawo karshen almajiranci da kuma yanda za’a kawo karshen bara da kananan yara keyi a jihar.

Gwamnan ya sanar da haka a wani taron kwana daya na wayar da kai akan illar yin bara da sakamakon ta wajen tabbatar da tsaro a kasa da haka gabatar a garin Kaduna ranar talata.

Gwamnan wanda ya waƙiltar da matar sa Hadiza El-rufai yana tabbatar ma yan jihar cewa gwamnati zata dauki wani mataki wajen tabbatar cewa an kawo karshen bara da yara kanana keyi kuma ya kara da cewa dole a kula yara don kuwa sune manyan gobe kuma abun alfahari ga iyayen su.

A nata jawabin, ministan almuran kasashen waje Hajiya Khadija Bukar tana cewa an shirya taron don samun shawarwari da samun mafita daga jama’a don kawo karshen bara a ƙasar baki daya.

Ministan tayi kira ga iyaye da su kula da yaran su kuma su tabbatar sun tarbiyar dasu kuma sun samar masu ilimi managarta.

A baya wakilin ECOWAS Ali Gubuci yayi ma ‘yan arewacin Nigerian gargadi da su tashi tsaye don tsira daga illar dake tare da bara inda yake cewa indai ba’a dau mataki ba zai haifar da abubuwa da dama masu illa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.