El-Rufa iya bayyana takaddar albashinsa a ranar Litinin, Afrilu 10, a mayar da martani ga wani ƙalubale daga kakakin majalisar waƙilai, Hon.Yakubu Dogara.
Gwamna ya bayyana ƙuri’un tsaro, karin bayanin albashi - ya na samun ribar N470,000 a kowane wata
Kakakin majalisar waƙilai, Yakubu Dogara ya ƙalubalanci El-Rufai ya bayyana albashin sa da kuma alawus bayan Gwamnan ya ce kasafin kuɗin NASS bai nuna gaskiya.
A cikakken bayani, da mataimakin gwamna na kafofin watsa labarai Samuel Aruwan ya saki, ya nuna cewa ya na samun ribar N470, 521,74 wata-wata.
Kashin na a haka :
Kudin shiga
Albashi : N185,308.75,
Alawus na wahala : N370,617.50
Gross Pay; N555,926.25,
PAYE: N85,404.5
Net Pay : N470,521.74
Ƙuri'un tsaro ta Gwamnan na 2017 N4.556bn. Wannan ya haɗa da siyar da kuma jona kamara na CCTV na Kulawa da Sanya ido, siyar Geo-position interceptor da gane wuri na GSM UMTS System domin daɗile / gano masu sata, 'GSM na kira da kuma siyan Drones / Unmanned Aerial Vehicles (UAV).
Satin da ya gabata, El-Rufai ya suka Majalisar Dokoki ta ƙasa (NASS), da cewa kasafin kuɗin su ta asa nuna gaskiya.
Ya nemi Majalisar su samar da ƙarin bayani a kan N115 biliyan na NASS kasafin kudi na 2016
A mayar da martani ga wannan, Dogara, ya ƙalubalanci El-Rufai ya nuna wa jama'a albashin sa da kuma ƙuri'un tsaro.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng