ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sanata ya kubuta daga hannun barayi da suka sace shi

A safiyar yau ne dan majalisar mai wakiltar jihar Kogi ta yamma ya sanar cewa yayi nasarar kubutowa daga hannun wadanda suka sace shi.

A wata sako da abokin aikin sa na majalisa Sanata Ben Bruce ya wallafa, yace barayin sun sace shi ne a dai unguwar gwagwalada dake nan garin Abuja  hanyar shi na zuwa zaman kotu kan tuhumar da ake masa.

A sakon da ya fitar a shafin sa na Twitter, dan majalisar yace sai da yayi sa'o'i 11 a daji cikin halin kunci mai firgitarwa.

Dan majalisar yayi ma Allah godiya bisa nasarar da ya samu na kara tsallakewa daga tarkon mahara.

ADVERTISEMENT

Ya kuma yi ma dinbim jama'a da suka yi masa addu'a tare da taya shi jaje godiya.

Batun sace shi ya faru ne bayan kwana daya da lamarin da ya faru a zauren majalisar dattawa inda sanatoci 15 suka sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Dino Melaye yana daya daga cikin yan majalisar da suka dauki matakin barin jam'iyar mai mulki a ranar.

Sanatan yana fuskantar tuhuma a kotu kan karar da aka shigar a kan sa na zargin goyon baya wasu yan fashi da makami da aka kama a jihar Kogi.

Kasancewa bai halarci zaman kotu domin sauraron kara sakamakon abun da ya faru, kotun ta daga ranar cigaba da sauraro zuwa ranar 9 ga watan Agusta na wannan shekarar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT