Pulse.ng logo
Go

A jihar kaduna Dandazon jama'a sun sauya sheka daga APC zuwa PDP, sunyi bikin kona tsinsiya

Anyi bikin tarbar su a garin Zonkwa dake karamar hukumar Zangon kataf ranar litinin 7 ga watan mayu

  • Published:
Dandazon jama'a sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kaduna play

Dandazon jama'a sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kaduna

Yanayi ya canza fuska a kudancin jihar Kaduna inda yayan jam'iyar APC sama da 5,000 suka sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP.

Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Kagarko da Kachia, Honarable Jagaba Adams ya jagoranci sauran jama'a wajen canza sheka.

Anyi bikin tarbar su a garin Zonkwa dake karamar hukumar Zangon kataf ranar litinin 7 ga watan mayu.

Anyi bikin kone tsintsiya bayan wasu yan APC sun sauya sheka zuwa PDP play

Anyi bikin kone tsintsiya bayan wasu yan APC sun sauya sheka zuwa PDP

(Facebook/rariya)

 

Manya jami'an PDP na kasa baki daya da na jiha sun halarci taron bikin ciki har da tsohon shugaban jam'iyar ta kasa, Sanata Ahmed Makarfi.

A jawabin sa, Sanata Makarfi ya gargadi su da su taimaka wajen tabbatar da manufar jam'iyar a jihar da ma kasar baki daya.

Shima shugaban jam'iya na jihar, Dakta Hassan Hyet yayi maraba da masu sauya sheka. Ya kara da yi ,masu  albishir da samun nasara.

Anyi bikin kone tsintsiya bayan wasu yan APC sun sauya sheka zuwa PDP play

Anyi bikin kone tsintsiya bayan wasu yan APC sun sauya sheka zuwa PDP

(Facebook/rariya)

 

Bayan ga taron bikin tarban su, wadanda suka canza akida sun gudanar da biki kona tsintsiya don nuna alamar barin APC.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement