Shahararren dan wasan barkawanci a dandalin fina-finan hausa ta Kannywood, Mustapha Naburiska, ya jaddada soyyayar da yake ma tsohon gwamnan  jihar Kano kuma dan majalisar dattawa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Ya bayyana cewa idan har akwai wata cuta da Allah ya dora masa, to ba ta wuce kaunar Kwankwasiyya ba, kuma ba ya fatan Allah ya yaye masa.

A wata hira da yayi da jaridar Rariya jarumin barkwacin ya karyata jita-jita dake yaduwa na cewa ya sauya sheka daga Kwankwasiyya zuwa Gandujiyya.

Jarumin ya bayyana cewa hotunan da ake ta yadawa cewa ya yi wa Gandujiyya mubaya'a, ba gaskiya ba ne, kawai sun hadu ne da mutanen gwamnatin Kano a wurin zaben shugabannin jam'iyyar APC na kasa da ake gudanar a Abuja kwanan baya. Kuma sun kira shi ne domin a gaisa kasancewar sa dan Kano.

"Sun kira ni ne muka gaisa, har suke zolaya ta cewa har yanzu na ki bin su a tafi tare a siyasa, sai nake ce musu ai siyasa kowa yana da ra'ayinsa. Don haka ni Kwankwaso zabina, kuma bai mu raba ni da shi", cewar jarumin.

Jarumin ya kara da cewa babu irin zawarcin da mukarraban gwamnan Ganduje ba sa yi masa don ganin ya dawo tafiyar Gandujiyya amma ya ki. Ya ce akwai wadanda har zagin cin fuska suke yi masa saboda ya ki karbar tayin tafiyar Gandujiyya.

Ya kara da cewa "Ni da Sanata Kwankwaso mutu-ka-raba. Domin ya yi min halacci. Kuma masu iya magana na cewa ruwan da ya dake ka shine ruwa".

Kai ga yanzu, tauraron wasan barkwanci shine ke rike da sarautar sarkin yakin kwankwaso wanda tafiyar kwankwasiyya ta nada shi.