Adam Zango daya daga cikin fitattun jarumai Kannywood dake nishadantr da alummar Nijeriya da ma na sauran kasashen waje.

Dagiya da jurewar sa ya kaisa ga zama gwanin arewa a dandalin nishadi.

Hakika yana daya daga cikin kashin bayan masana'antar fim kuma kwarewar sa ya shafe sama da shekaru 15.

Ga wasu abubuwa bakwai da ya kamata masu kuratu su sani game da wanin jarumi wanda har yanzu tauraron sa ke haskawa:

1. Haihuwar sa

An haifi Adam Zango a garin Zangon Kataf dake nan jihar Kaduna cikin shekarar 1985. Ya koma garin Jos tare da iyayen sa sakamakon rikicin da ya barke a Zangon kataf shekarar 1992.

Shi dai Zango baya boye matsayin sa game da karatun sa domin kuwa babu wata kwararriyar takarda karatu da samu.

2. Ya dakatar da karatun sa domin cinma burin sa na zama jarumi

Ya sha bayyana wa masu yi masa gyaran turanci cewa shi bai yi karatu ba kuma iya turanci ba shi bane matakin da zai tabbatar da nasarar dan Adam a duniya.

Basirar sa da dagiyar sa ya kai shi ga matsayin da yake yanzu.

3. Kwarewar sa

Adam Zango ya kware sosai a bangaren wasan kwaikwayo bayan haka akasarin jama'a sun sani cewa ya kware a fannin waka.

hakazalika jarumin yayi fice a fannin rawa.

4. Iyalen gidansa

Jarumin shirin "Gwaska" yana da mata uku a halin yanzu ciki har yar jamhoriyar Kamaru wacce ya aura cikin shekarar 2015.

Sai dai a baya ya saki wasu matan da ya aura, lamarin da ya sa ake yi masa kallon mai auri-saki, ko da ya ke ya sha musanta hakan.

Yara kuwa, Zango yana tara su da dama ciki har babban dan shi Haidar wanda ke bin sahun sa a fannin waka.

5. Abincin da ya fi so

Kamar yadda dan uwar sa ya bayyana hirar shi da jaridar Daily trust Adam Zango baya wasa da abinin gargajiya.

Yana lale maraba da duk wani nau'in abincin arewa amma mafi soyuwa a gare shi shine tuwon Semovita da miyan kuka.

Masu karatu daya daga cikin abun dake sanya shi murmushi shine idan har aka yi masa albishir da abinci da yafi so.

6. Me ke sanya shi fara'a

Babban abun dake haifar da farin ciki a wajen sa shine barkwanci. Wasannin barkwanci na cikin abubuwan da yafi a rayuwa.

7. Abun dake bata masa rai

Babban abun dake haifar da bakin ciki a gare shi kamar yadda Lawal Idiya Usman shine munafurci da masu yi masa karya a bayan fage.

Bayan haka jarumin mutum ne wanda ke da saukin mu'amala kana shi mutum ne wanda baya son fitina.