Pulse.ng logo
Go

Raya watan Ramadan Dan wasa ya rabawa mabuka kayan abinci da kudi

Dan wasan wanda ke taka leda da kungiyar CSKA Moscow dake Rasha, ya bi sahun masu fitar da arzikin da Allah yayi masu wajen ciyar da jama'a domin raya wannan watan mai albarka.

  • Published:
Dan wasa y raba kayan abinci ga mabukata play

Dan wasa y raba kayan abinci ga mabukata

(Instagram/ahmedmusa)

Shahararen dan wasan kwallon tawagar super eagles ta Nijeriya, Ahmed Musa yayi ma wasu mabukata aikin alheri inda ya raba masu kayan abinci da kudi.

Daya daga cikin ayyukan da ake kwadayi musulmi yayi a cikin watan ramadan shine faran ta ran mara sa galihu ta hanyar tallafa masu da kayan abinci da kyuatatawa domin suma su gudanar da ibada kamar sauran musulmai.

When u have that good heart @ahmedmusa718

A post shared by Ahmed Musa Sport Centre (@ahmed_musa_sport_centre718) on

 

Dan wasan wanda ke taka leda da kungiyar CSKA Moscow dake Rasha, ya bi sahun masu fitar da arzikin da Allah yayi masu wajen ciyar da jama'a domin raya wannan watan mai albarka.

Dan wasan gaban tawagar Leicester wanda aka bada aron shi zuwa CSKA Moscow, ya bayar da buhunan shinkafa mai dauke da hoton shi tare da raba kudi ga mabukata domin suma su amfana da arzikin da Allah yayi mashi.

play (Instagram/ahmedmusa718)

 

Tsohon dan wasan kungiyar Kano Pillars yayi hakan ne a harabar wajen motsa jiki da ya gina a garin kano.

play (Instagram/ahmedmusa718)

Dan kwallon ya wallafa hotunan sanda ya  rabon ke gudana a shafin sa na Instgram inda dinbim ma'abotan shafin sa suke ta masa ruwan godiya bisa alherin da yayi.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.