ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan shugaban kasa zai yi watanni a gidan yari kan laifin satar waya

An yanke ma Frederick Chiluba Jr. hukuncin ne a zaman kotun da aka yi ranar laraba 16 ga watan mayu a birnin Lusaka.

Kotun tace dan tsohon shugaban kasar Zambia, Frederick Chiluba zaiyi wata takwas a gidan kaso bisa ga laifin da ya aikata.

An yanke ma Frederick Chiluba Jr. hukuncin ne a zaman kotun da aka yi ranar laraba 16 ga watan mayu a birnin Lusaka.

Kamar yadda majiya BBC ta fitar, an kama shi da laifin ne bayan ya saci waya kirar Samsung S7 na wata mai suna Brenda Chisa wanda aka yi ma kudi da dala $843. Bayan ga haka yayi musayyar ta domin samun miyagun kwayoyi.

Lamarin ya faru ne a cikin watan satumba na shekarar 20117 kuma kamar yadda Brenda Chisha ta shaida ma kotu "tayi mamakin abun da tsohon abokin huldar ta" yayi.

ADVERTISEMENT

A cewar ta ya amshi wayar a hannun ta ne cikin wasa inda daga bisani ya face daga ganin idon ta.

Labarin hukuncin da aka zartar kan laifin sa ya zama abun muhawara a kafafen sada zumunta inda jama'a da dama na mamakin yadda dan tsohon shugaban kasa zai samu hukunci zama a gidan wakafi na tsawon watanni kan laifi sata.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT