Dino Melaye zai bada amsar tambayoyi ne kan zargin daukar nauyin wasu yan tawaye da aka kama kwanan baya a jihar Kogi.
Dan majalisa yayi saduda, ya amince da ziyartar ofishin yan sanda domin bada amsar tambayoyi
Dino Melaye zai bada amsar tambayoyi ne kan zargin daukar nauyin wasu yan tawaye da aka kama kwanan baya a jihar Kogi
Bayan ya kwashi lokuta da dama kin amincewa da gayatar da yan sanda sukla yi masa, dan majalisar ya shiga hannun jami'an tsaron filin jirgin sama na Abuja yayin da yake kokarin tafiya kasar Morocco domin gabatar da wani aiki da gwamnatin tarayya ta tura shi.
Jim kadan bayan kama shi, ya sanar cewa an sake shi ya kuma sanar cewa yan sanda sunyi ma gidan sa kawanya tare da hana shiga da fita.
Yana mai cewa, duk cikin shirin saka masa tarko, rundunar yan sanda sun janye jami'an dake tsaran shi.
Sakamakon kai-kawo dake faruwa tsakanin shi da jami'an tsaro wanda ya zama abun muhawara a kakafen sada zumunta, daga karshe dai sanatan ya amince da ziyartar ofishin yan sanda.
Ya rubuta a shafin sa na twitter "Yau zan gabatar da kaina gaban yan sanda, shirin da nike na fadan gaskiya tare da kare hakkin talakan Nijeriya tana nan daram-dam-dam. Zamu yi nasara".
Dino Melaye yana dayta daga cikin yan siyasa da ake dama
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng